Isa ga babban shafi

Al Shebaab ta kashe Sojojin Somalia 11 a harin da ta kai sansaninsu

Mayakan kungiyar Al Shebaab sun farmaki sansanin Sojin Somalia tare da kashe dakaru 11 dai dai lokacin da kasar ke ikirarin fatattakar mayakan ‘yan ta’addan.

Sojojin Somalia 11 suka mutu a harin na yau.
Sojojin Somalia 11 suka mutu a harin na yau. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Da safiyar yau talata ne ‘yan ta’adda suka farmaki sansanin na Hawadley da ke arewacin Somalia mai tazarar kilomita 60 daga Mogadishu babban birnin kasar harin da wasu majiyoyi ke cewa alkaluman mamatan za su iya karuwa sakamakon tarin wadanda suka jikkata.

A jawabinsa ta gidan rediyon kasa, babban hafson Sojin Somalia ya bayyana dakarun da suka mutu a farmakin na yau a matsayin shahidai da suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasa.

Kwamandan rundunar sa kai da ke taimakawa Sojojin na Somalia a yaki da ‘yan ta’addan Mohamed Osman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Sojoji 11 suka kwanta dama nan take baya ga wasu da yawa da suka samu muggan raunuka.

A cewar Mohamed Osman ’yan ta’addan sun makare wata mota da bama-bamai wadda suka yi amfani da ita wajen kai harin kunar bakin wake gabanin bin bayanta da hare-harbe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.