Isa ga babban shafi

Mutane 19 sun mutu a harin bama-baman da aka kai a Somalia

Akalla mutane 19 suka mutu, wasu da dama kuma suka samu raunuka bayan wasu jerin hare-hare da aka kai a garin Mahas da ke yankin tsakiyar Somalia.

Wani  hari bam da mayakan Al Shabaa ta kai a birnin Mogadishu a watan Oktoban shekarar 2022.
Wani hari bam da mayakan Al Shabaa ta kai a birnin Mogadishu a watan Oktoban shekarar 2022. ABDIHALIM BASHIR via REUTERS - ABDIHALIM BASHIR
Talla

Bayanan da suka fara fita da fari sun nuna cewar mutane 9 suka mutu, a hare-haren.

Shaidun gani da ido sun ce an tarwatsa bama-baman da aka kai harin da su ne a kusa da wani gidan cin abinci, wanda ba shi da nisa daga ginin hedikwatar gwamnatin yankin.

Wani jami’in tsaron Abdullahi Adan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, ‘yan ta’adda sun yi amfai da motoci makare da bama bamai ne wajen kai harin da safiyar ranar Larabar da ta gabata, wanda kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai wa.

Garin Mahas yana yankin Hiran ne da tsakiyar Somalia in da sojojin kasar ta kaddamar da gagarumin farmaki akan mayakan Al-Shebaab mai alaka da Al Qaeda a shekarar da ta gabata.

Watanni kalilan bayan hawansa mulki, shugaban Somalia Hassan Shiekh Mahmud ya yi shelar kaddamar da yaki nan gaba gadi kan kungiyar Al-Shabaab da ta shafe shekaru 15 tana kokarin kifar da gwamnati a kasar ta Somalia.

A watan Yulin da ya gabata, wasu mayakan sa-kai daga kabilar Macawisley suka kaddamar da yaki kan mayakan Al-Shebaab a sassan yankin tsakiyar Somalia, daga bisani  kuma shugaba Mahmud ya aike da sojoji domn taimakawa mayakan sa-kan.

A ‘yan watannin baya bayan kuma, hadin gwiwar sojoji da mayakan sa-kan na Macawisley ya samu nasarar kwato yankuna masu yawan gaske daga karkashin mayakan Al-Shabaab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.