Isa ga babban shafi

Al Shebaab ta shafe sa'o'i 6 tana kai farmaki kan Otal din Kisimayo

Akalla mutane 9 aka kashe, tare da jikkata wasu 47 ranar Lahadi, a wani hari da aka kai kan wani Otal da ke birnin Kismaayo a kudancin Somalia, farmakin da kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakinsa.

Otal din Asasey, daya daga cikin Otal-Otal din da suka fuskanci hare-haren mayakan Al Shebaab a birnin Kisimayo da ke kudancin kasar Somalia.
Otal din Asasey, daya daga cikin Otal-Otal din da suka fuskanci hare-haren mayakan Al Shebaab a birnin Kisimayo da ke kudancin kasar Somalia. © AP
Talla

Birnin na Kisimaayo mai tashar jiragen ruwa shi ne na baya-bayan nan da ya fuskanci hare-haren kungiyar Al Shebaab mai alaka da Al-Qaeda, wadda ta fi mayar da hankali wajen kai hare-hare a birnin Mogadishu da kuma yankin tsakiyar kasar Somalia.

Bayanai sun ce, mayakan na Al Sheebaab sun kaddamar da harin na ranar Lahadi ne da misalin karfe 12:45 na rana wato 9:45 na safe agogon GMT, lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta afkawa kofar shiga Otal din Tawakal. Sai kuma da aka shafe sa’o’i shidda kafin jami’an tsaro su kashe mahara uku da suka kai farmakin, yayin da ragowar guda ya tarwatsa damarar bam din da ke jikinsa.

Ministan tsaron yankin Jubaland Yusuf Hussein Osman ya shaida wa manema labarai cewa, daga cikin wadanda suka jikkata a harin akwai daliban da suka tashi daga wata makaranta da ke kusa da inda aka kai farmakin.

‘Yan sandan Somalia sun ce fararen hula ne suka fi mu’amala da Otal din da aka kaiwa hari, sai dai kungiyar Al-Shabaab ta ce mambobin gwamnatin yankin Jubaland, inda birnin Kismayo yake, suna ganawa cikin Otal din, a lokacin da mayakanta suka kai farmakin na sa’o’i 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.