Isa ga babban shafi

Harin bama-bamai ya kashe mutane a Somalia

Akalla mutane uku sun rasa rayukansu, sannan da dama sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai da mota makare da bama-bamai da kuma harbe-harben bindiga kan wani otel da ke birnin Kismayu na kasar Somalia.

Wasu daga cikin mayakan Al-Shebab a Somalia
Wasu daga cikin mayakan Al-Shebab a Somalia AFP/TOPSHOTS/STRINGER
Talla

An fara jin karar harbe-harben bindiga jim kadan da fashewar bama-bamai da ke cikin motar wadda ta  yi karo da babban kofar shiga cikin otel din na Tawakal, yayin da mayakan Al-Shebab masu alaka da Al-Qaeda suka dauki alhakin kaddamar da farmakin.

Rahotanni na cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kan gudanar da wani taro a otel din kan yadda za a murkushe mayakan na  Al-Sshebab a kasar ta Somalia.

Har yanzu dai kungiyar ta Al-Shebab na rike da ikon wasu yankuna na birnin na Kismayu mai cike da hada-hadar kasuwanci a yankin kudancin Somalia.

Sojojin kasar sun yi nasarar fatattakar mayakan na Al-shebab daga birnin a shekara ta 2012, birnin da ke samar wa mayakan kudaden shiga domin sayen makamai.

Ko a shekara ta 2019, sai da mayakan suka kaddamar da makamancin wannan harin da ya kashe mutane 26 a Kismayu.

Har yanzu dai mayakan Al-Shebab ba su daddara ba a yunkurinsu na ganin sun kifar da gwamnatin Somalia domin kafa irin tasu gwamnatin, yayin da suka kashe dubban 'yan kasar a jerin hare-haren da suka kaddamar cikin shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.