Isa ga babban shafi

Gwamnatin Somalia ta gargadi 'yan kasuwa kan biyan Al-Shebaab haraji

Gwamnatin Somalia ta yi barazanar sanya takunkumi ga ‘yan kasuwar da ke biyan kudaden haraji ga kungiyar Al-Shabaab, a wani matakin dakile makudan kudade da masu kaifin kishin Islaman ke amfani da su wajen tafiyar da kungiyar dake kaddamar da munanan hare-hare kan gwamnati.

Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011
Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011 AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antu ta Somalia ta ce gwamnatin za ta yi amfani da cikakken ikonta kan 'yan kasuwar da ke biyan kungiyar dake kawance da Al-Qaeda, wanda masana suka ce tana tara miliyoyin daloli ta hanyar tsarin haraji daga ‘yan kasuwa.

Ma'aikatar ta ce duk wani dan kasuwa ko kamfani da aka samu ya biya ko hada hannu da Al-Shabaab ta kowace hanya "za ya fuskanci tuhumar shari'a" ciki har da kwace lasisin cinikayya da gwamnati ta ba su.

"Duk dan kasuwan da ya bi umarnin da 'yan ta'addan suka bayar, kuma ya biya su kudaden shiga, ba za a sake bari ya sake yin kasuwanci a Somaliya ba," in ji ma'aikatar cikin wata wasika ga 'yan kasuwa.

"Duk kamfani da aka samu ya na taimakawa 'yan kungiyar Al-Shabaab, ko kuma ke daukar nauyin hajarsu, gwamnati za ta kwace kadarorinsa da suka hada da gidaje."

Sama da shekaru 15 ne kungiyar al-Shabaab ke kokarin hambarar da gwamnatin tsakiyar kasar a Mogadishu, kuma a kai a kai tana kai munanan hare-haren bama-bamai da kuma kai hare-hare kan fararen hula da sojoji.

Duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na karya logon kungiyar, mayakan sun mamaye yankunan karkara, kuma suna karbar haraji a yankunan da ke karkashin ikonsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.