Isa ga babban shafi

Harin bam ya kashe mutane kusan 100 a Somalia

Akalla mutane 100 ne suka mutu a Somalia,ciki har da yara kanana a wani harin bam da aka kai da motoci biyu a kan wata hanya mai cike da jama'a a tsakiyar Mogadishu babban birnin kasar a jiya asabar.

Harin bam a Somalia
Harin bam a Somalia ABDIHALIM BASHIR via REUTERS - ABDIHALIM BASHIR
Talla

An kashe mutane 100 tare da jikkata 300, in ji shugaban kasar  Hassan Sheikh Mohamushi bayan ya ziyarci inda aka kai harin.

Motoci biyu makil da bama-bamai sun tashi cikin mintuna kadan da rana a kusa da mahadar Zobe mai cunkoson jama'a, daga baya aka kuma ji  harbe-harbe kan ma'aikatar ilimi ta Somalia.

Bama-baman sun farfasa tagogin gine-ginen da ke kusa da wurin, lamarin da ya haifar da hayaki da kura a wannan wuri.

An kai harin ne a daidai mahadar jama’a inda wata babbar mota ta fashe a ranar 14 ga watan Oktoba shekarar 2017, inda mutane 512 suka mutu, sama da 290 suka jikkata.

A wuri daya ne kuma mutanen da ba su ji ba ba su gani ba  wadanda abin ya shafa, in ji Shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamushi.

shugaban ya na mai cewa ‘ba daidai ba ne, In sha Allahu, hukumomin za su taka rawar da ta dace wajen murkushe masu aikata irin wannan kazamin aiki.

Wannan nau'in harin, hukumomin kasar Somaliya na alakanta shi da mayakan Al-Shabaab da ke kai hare-hare akai-akai a babban birnin kasar da manyan biranen kasar Somaliya.

Tun a shekara ta 2007 ne kungiyar Al-Shebab mai alaka da Al-Qaeda ke yaki da gwamnatin tarayya da ke samun goyon bayan kasashen duniya.

An kore yan kungiyar daga manyan biranen kasar Somalia  ciki har da Mogadishu a shekara ta 2011.

A cewar wani ganau, Abdirahman Ise, akwai mutane da yawa a kan hanyar tare da ma'aikata a lokacin fashewar farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.