Isa ga babban shafi
Somalia

Al Shebab ta kai hare hare a Somalia da Kenya

Kungiyar Al-Shebab ta kaddamar da farmaki kan sansanin sojin Somalia, inda ta hallaka jami’in tattara bayanan sirri, tare da kasha mutane 12 a wani hari na daban da ta kai a Kenya.

Al shebab ta kai harin kunar bakin wake a sansanin dakarun AMISOM da ke garin Beledweyne cikin Somalia
Al shebab ta kai harin kunar bakin wake a sansanin dakarun AMISOM da ke garin Beledweyne cikin Somalia REUTERS
Talla

Al-shebab ta kaddamar da jerin hare-haren ne cikin sa’oi 24 a Somalia da kuma kan iyakar Kenya.

Mai magana da yawun kungiyar, Abu Musab ya ce, su suka yi amfani da katuwar mota makare da bama-bamai wajen kai wa sansanin sojin na kungiyar kasashen Afrika harin, kuma ya cesojoji 17 suka kashe.

Rundunar AMISON wadda ta kunshi sojojin kasashen Kenya da Djibouti da Uganda da Habasha, ta ce ‘yan ta’adda 10 ne suka mutu a farmakin.

Al shebab ta sake kai wani farmakin na daban a wani Otel da ke garin Mandera na Kenya, in da ta kashe mutane 12 kamar yadda maj ‘yan sanda ta sanar.

Al Shebab dai wadda a can baya ta kame wurare da dama a Somalia, na bukatar hanbarar da gwamnatin Mogadishu da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya.

Sabon harin da kungiyar ta kai, na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin Somalia, wanda kuma zai kai ga zaben shugaban kasa da zai ci gaba da gina kasar bayan ta yi fama da rikice-rikice na tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.