Isa ga babban shafi

Mutane 4 sun mutu a wani otel da Al-Shabaab ta wa kawanya a Somalia

Akalla mutane 4 ne suka mutu a harin da kungiyar Al-Shabaab ke ci gaba da kai wa wani otel din da suka wa kawanya a Mogadishu, babban birnin Somalia tun daga daren Lahadi zuwa Litinin din nan.

Tun a shekarar 2007, Al-Shabaab, mai alaka da  Al-Qaeda ke kokarin kifar da gwamnatin Somalia.
Tun a shekarar 2007, Al-Shabaab, mai alaka da Al-Qaeda ke kokarin kifar da gwamnatin Somalia. AFP/File
Talla

Har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ana iya jin kararrakin harbe harbe da fashewar abubuwa, sa’o’i 12 bayan da ‘yan ta’addan suka kutsa otel din da ke kusa da fadar shugaban kasar.

Mohamed Dahir, wani jami’i daga hukumar tsaron kasar ya ce ‘yan ta’addan sun jibge kansu ne a wani dakin otel din na Villa Rose, a yayin da dakarun gwamnati suka yi musu kawanya.

Ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 4, inda ya kara da cewa an ceto da dama daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka ritsa da su a otel din, yana maai cewa nan ba da jimawa ba komai zai daidaita.

Villa Rose, otel ne da akasarin ‘yan majalisar dokokin Somalia ke yawaita zuwa, kuma yana yankin tsakiyar babban birnin kasar, Mogadishu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.