Isa ga babban shafi

Amurka ta kai hare-haren sama kan mayakan Al Shebaab a Somalia

Amurka ta kaddamar da hare-haren jiragen sama da suka lalata makaman da mayakan Al-Shebaab suka sace a kusa da sansanin sojin Kungiyar Tarayyar Afrika da ke Somalia. 

Wasu mayakan Al Shebaab.
Wasu mayakan Al Shebaab. ASSOCIATED PRESS - Mohamed Sheikh Nor
Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, mayakan Al-Shebaab masu alaka da Al-Qaeda suka kai hari kan sansanin Bulo Marer mai tazarar kilomita 120 daga yankin kudu maso yammacin babban birnin Mogadishu. 

Sansanin dai na dauke da sojojin Uganda a lokacin da aka kai harin, yayin da wata sanarwar gwamnatin kasar ke tabbatar da cewa, wasu daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu ba tare da ta bayar da adadi ba. 

Yanzu haka rundunar sojin Amurka da ke Afrika ta ce, ta lalata makamai da sauran kayayyakin yakin da Al-Shebaab ta sace. 

Dakarun na Amurka sun ce sun kai harin ne tare da taimakon gwamnatin Somalia da sojojin wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika da aka fi sani da ATMIS. 

Mayakan na Al-Shebaab sun yi amfani da wata mota makare da bama-bamai wajen kai harin kan sansanin sojin kamar yadda kwamandan rundunar sojin Somalia ya tabbatar wa AFP. 

 Al-Shebaab ta shafe sama da shekaru 15 tana kaddamar da farmaki a kasar ta Somalia da ke kuryar gabashin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.