Isa ga babban shafi

Kenya da Somalia sun bude iyakarsu ga juna shekaru 12 bayan kullewa

Kasashen Kenya da Somalia sun amince da sake bude iyakokinsu ga juna bayan shafe fiye da shekaru goma a kulle wanda ke da nasaba da matsalar tsaron da ta tsananta a Mogadishu, lamarin da ma'aikatar cikin gida a Nairobi ke cewa zai kawo karshen takun sakar tsawon shekaru da kasashen biyu makwabtan juna suka shafe suna fuskanta. 

Ministan harkokin wajen Somalia,Dr. Mohamed Ahmed Sheikh Ali tare da takwaransa na Kenya Dr. Kithure Kindiki.
Ministan harkokin wajen Somalia,Dr. Mohamed Ahmed Sheikh Ali tare da takwaransa na Kenya Dr. Kithure Kindiki. © Florence Kiwuwa
Talla

A watan Oktoban 2011 ne aka rufe kan iyakar biyo bayan yawaitar hare-haren da mayakan Al-Shabaab ke kai wa Kenya daga Somalia, wadanda suka shafe fiye da shekaru 15 suna tayar da kayar baya ga gwamnatin Mogadishu ta hanyar tayar da bama-bamai a hare-haren ta'addanci da suke kaiwa sassa da ma'aikatun gwamnati.  

 A watan Yulin shekarar da ta gabata ne kasashen biyu suka sanar da shirin sake bude iyakar a tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban Kenya na lokacin Uhuru Kenyatta da takwaransa na Somalia Hassan Sheikh Mohamud amma ba a kai ga cimma jituwa ba. 

Ministan cikin gidan Kenya Kithure Kindiki ya bayyana yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na Somalia Mohamed Ahmed Sheikh Ali cewa, kasashen biyu za su yi aiki tare a fannin tsaro, kasuwanci da zirga-zirgar jama'a da sauran hanyoyin yin hadin gwiwa tsakaninsu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.