Isa ga babban shafi

Amurka za ta bada dala miliyan 10 ga wanda ya gano maboyar jagoran Al Shebaab

Amurka ta yi shelar tayin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayyana maboyar mutumin da ya kitsa harin Otel din Kenya na shekarar 2019 wanda ya kashe mutane fiye da 20 ciki har da Amurkawa da kuma jami’an tsaro.

Harin Otel din birnin Nairobi a Kenya.
Harin Otel din birnin Nairobi a Kenya. Photo: Kabir Dhanji/AFP
Talla

Amurka ta bayyana sunan Mohamoud Abdi Aden a matsayin wanda ya kitsa harin na ranar 15 ga watan Janairun 2019 wanda kuma shi ne jagoran Mayakan Al-Shebaab a Somalia.

Amurka ta bayyana cewa Abdi Aden ya kitsa mabanbantan hare-haren da suka kashe tarin jama’a a kasashen da ke makwabtaka da Somalia.

Yayin harin na ranar 15 ga watan Janairun a shekaru 4 da suka gabata dai mayakan Al Shebaab sun yiwa Otel din DusitD2 da ke birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar kawanya, suka kuma shafe sa’o’I 20 suna kaddamar da hari tare da musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro a cikin Otel din.

Yayin harin dai wanda ya kashe mutane 21 ciki har da wasu Amurkawa jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka dukkanin maharan.

Jakadar Amurka a Nairobi Meg Whitman ta shaidawa manema labarai a birnin Nairobi cewa a shirye suke su biya dala miliyan 10 ga duk wanda ya gano maboyar dan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.