Isa ga babban shafi

Shugaban Al Shebaab ya bukaci kai hari kan muradun Amurka da Faransa

Shugaban kungiyar Al Shebaab dake kai hare hare a kasar Somalia Ahmed Diriye ya bukaci kai hari kan muradun kasashen Amurka da Faransa dake Djibouti kasa da makwanni biyu kafin gudanar da zaben shugaban kasa.

Mayakan Al Shebab a wani lokaci da suke gudanar da sitiri
Mayakan Al Shebab a wani lokaci da suke gudanar da sitiri (Photo : Reuters)
Talla

A sakon bidiyo da ya fitar, Diriye da ake kira Ahmed Umar Abu Ubaidah ya cacaki shugaban kasar Djibouti Ismaila Omar Guelleh wanda ke karagar mulki tun daga shekarar 1999 kuma ake hasashen zai lashe zaben da za’ayi ranar 9 ga watan Afrilu domin yin wa’adi na 5.

Shugaban Al Shebaab ya zargi shugaban Djibouti da mayar da yankin dandalin sojin kasashen duniya wanda ake amfani da su wajen shirya kai hari kan Musulman dake Gabashin Afirka.

Diriye ya bukaci magoya bayan sa da su mayar da muradun Amurka da Faransa a yankin wajen kai hare haren su.

Kasar Djibouti na dauke da sojojin Faransa 1,500 tare da na kasar Amurka kusan 4,000, yayin da suma kasashen Japan da Italia ke da nasu sansanonin sojin.

Kasar China ta mallaki tashar jiragen ruwa da sansanin soji tun daga shekarar 2017.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.