Ambaliya ta raba sama da mutane dubu 200 da muhallansu a Somalia
Kimanin mutane dubu 200 ne suka rabu da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa, bayan da kogin Shabelle ya zarce gabarsa har ya mamaye tituna da gidaje.
Wallafawa ranar:
Ala tilas mazauna garin Beledweyne a yankin Hiran na kasar suka bar gidajensu, inda aka gansu dauke da kayayyakinsu a kansu, suna tafiya a kan titunan da ambaliyar ta mamaye.
Mataimakin gwamnan yankin, Hassan Ibrahim Abdulle ya ce mutane 3 sun mutu sakamakon wannan ambaliyar.
Masana sun ce ana samun karuwar yayanyi mai tsanani irin wannan ne sakamakon sauyin yanayi da ake fuskanta, kuma nahiyar Afrika, wadda kasonta na ayuyukan da ke haddasa sauyin yanayi shine mafi kankanta, ta fi fama da tasirinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu