Isa ga babban shafi

Kungiyar 'yan tawayen Abzinawa a Mali ta zargi Sojoji da kai mata hari

Tsofaffin ‘yan tawayen Abzinawa da ke Arewacin Mali, sun zargi sojojin kasar da kai musu hari ta sama a yankin da su ke, lamarin da ke kara haifar da barazana a tsakanin bangarorin. 

Wasu Sojin Mali.
Wasu Sojin Mali. REUTERS/Joe Penney
Talla

A zantawar kakakin kungiyar 'yan tawayen Abzinawan da kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, ya ce sojojin Mali sun kai musu hari ne a Anefis da ke yankin Kidal, duk da dai bai bayyana irin barnar da harin ya yi musu ba. 

Wani zababben dan siyasa daga yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kai harin, amma shi ma bai yi cikakken karin haske akan irin bannar da harin ya yi ba. 

Sai dai a martanin da Sojojin na Mali su ka yi ta dandalin sada zumunta sun bayyana cewa an kai harin na Anefis kan wasu gungun ‘yan ta’adda, da ke kokarin kai wa fararen hula da sojoji hari. 

A shekarar 2012 ne kungiyar Abzinawa ta faro tawayen da ya kai ga fantsamuwar ayyukan ta a kasashen Nijar da Burkina Faso, kafin nasarar cimma yarjejeniyar sulhu da su a shekarar 2015 da ya kawo karshen hare-haren su. 

Sai dai a baya-bayan nan ne alaka ta sake tsami tsakanin kungiyar da sojojin da ke mulki a Mali bayan kudirin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar da kungiyar ke cewa ya yi karantsaye ga yarjejeniyar da ke tsakaninta da gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.