Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kwace iko da yankuna masu yawa a arewacin Mali- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa cikin kasa da shekara guda mayaka masu ikirarin jihadi a Mali sun yi nasarar kwace iko da fiye da ninkin yankunan da suke hannunsu a baya, lamarin da ke nuna gazawar gwamnatin sojin kasar karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita.

Wasu mayaka masu ikirarin jihadi a Mali.
Wasu mayaka masu ikirarin jihadi a Mali. © SOULEYMANE AG ANARA / AFP
Talla

A rahoton da ya fitar, wani jami’in majalisar da ya gudanar da bincike kan ayyukan ta’addanci a Mali, ya bayyana yiwuwar kungiyoyin da ke biyayya ga ISIS da Al-Qaeda su cika kudirinsu na kwace iko da kasar kamar yadda suka kudirta yi a shekarar 2012.

A cewar rahoton wanda majalisar ta fitar a karshen mako, yarjejeniyar da aka cimma wadda ta kai ga aje makaman wasu mayaka masu ikirarin jihadi tare da sanyo su cikin al’umma ya bai wa kungiyoyi masu alaka da Al-Qaeda damar sake samun gindin-zama a Mali.

Rahoton ya ce cikin kasa da shekara guda kungiyar ISGS ko kuma Islamic State in the Greater Sahara ta kwace iko da fiye da rubanyen yankin da take iko da shi a Lardin Gao na arewacin Mali, haka zalika kungiyar JNIM mai biyayya ga al-Qaeda.

Rahoton ya bayyana yadda mayakan ISIL ke ci gaba da matsa kaimi wajen kai muggan hare-haren a yankunan gabashin Menaka da Ansongo na arewacin Gao.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.