Isa ga babban shafi

Amurka ta kakabawa wani kwamandan RSF a Sudun takunkumi

Amurka ta kakabawa kwamandan rundunar dakarun sakai na RSF a Sudan Abdel-Rahim Hamdan Dagalo takunkumi, bisa zarginsa da laifukan cin zarafi da take hakkin bil adama a rikicin da suka kwashe watanni suna yi da sojojin Sudan.

Hoton da aka ɗauka daga faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na Rundunar Sojojin Sudan ta Rapid Support Forces (RSF) a ranar 28 ga watan Yuli, 2023.
Hoton da aka ɗauka daga faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na Rundunar Sojojin Sudan ta Rapid Support Forces (RSF) a ranar 28 ga watan Yuli, 2023. AFP - -
Talla

A cikin wata sanarwa da baitulmalin Amurka ta fitar wannan Laraba ta ce ta sanya takunkumi kan Abdel-Rahim, wanda babban kwamandan soji ne kuma dan'uwa ga Mohammed Hamdan Dagalo, wanda shi ne shugaban rundunar dakarun kai daukin gaggawa da aka zargi da jagorantar wani gungun sojoji da ke da alhakin kisan kiyashin kan farar hula da kashe-kashen kabilanci da kuma lalata da mata.

Rikicin Sudan

Kasar Sudan ta fada cikin rudani kusan watanni biyar da suka gabata, bayan da aka dade ana takun saka tsakanin sojoji karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah Burhan, da kuma kungiyar RSF wanda ya rikide zuwa yakin basasa a kasar.

A cewar sanarwar na ranar Laraba, takunkumin zai toshe duk wasu kadarori mallakar Abdel-Rahim dake kasar Amurka.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa, Amurka ta kuma sanya takunkumin hana shiga kasar ta ga wani kwamandan kungiyar RSF, wato Abdul Rahman Juma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.