Hare-haren jiragen saman yaki ya kashe mutane 40 a wata kasuwar Sudan
Akalla mutabe 40 ne suka mutu, kana gwammai suka samu raunuka a yau Lahadi, sakamakon wani hari da aka kai ta sama a wata kasuwa a ke babban birnin Sudan, Khartoum, a yayin da yakin da ake a kasar ke daf da cika watanni 5.
Wallafawa ranar:
Wannan adadi na nuni da cewa harin shine guda 1 mafi muni da aka taba kaiwa tun da wannan yaki ya barke a watan Afrilu, sakamakon rashin jituwa tsakanin sshugabann rundunar sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa mai jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, Mohamed Hamdan Daglo.
Rahotanni sun ce da misalin karfe 5 da rabi agogon GMT jirgin saman yaki na sojin Sudan ya yi luguden wuta a yankin kasuwa Quoro.
Wata kungiya da ke bada gudummawa ga fararen hula a yaayin wannan yaki ta ce adadin mamata na iya karuwa kowane lokaci daga yaanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu