Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Morocco ya kusa 2,500

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar girgizar kasar da ta faru a Morocco, ya zarce dubu 2 da dari 5, a dai dai lokacin da kasar ke naman gudunmuwar kasashe don kubutar da ragowar mutanen da ke makale a karkashin burabuzai.

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar girgizar kasar da ta faru a Morocco, ya kai dubu 2 da dari 5.
Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar girgizar kasar da ta faru a Morocco, ya kai dubu 2 da dari 5. REUTERS - ABDELHAK BALHAKI
Talla

Girgizar kasar wacce ta kasance mafi muni a tarihin kasar tun bayan ta shekatat 1960, ta afku ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta hallaka mutane dubu biyu da dari 4 da 97 sannan wasu da dama suka jikkata.

A cewar wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, sun ce sama da mutane dubu dari uku ne girgzar kasar mai karfin maki 6.8 ta shafi, inda ta lalata gidaje da wuraren tarihi tare kuma da sanya dubban mutane kwana a bakin hanya.

Kasar ta Morocco ta aminci da bangaren agajin sojojin Spain, ya jagoranci mai kulada al’amuran kai daukin gaggawa da kuma aikin jinkai daga kasashen waje gameda lamarin.

Tun a ranar Lahadi ne sojojin na Spain da ke da kwarewa wajen abinda ya shafi yaki da annoba, suka isa kasar ta Morocco don taimakawa wajen kubutar da wadanda iftila’in ya shafa.

Kasashe da kuma kungiyoyi da dama ne su ka bayyana kudurinsu na taimakawa Morocco kan wannan iftila’in da ya sameta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.