Isa ga babban shafi

Gwamnan jihar Kogi ya musanta yunkurin hallaka shi

Gwamnan jihar Kogi a Najeriya Yahaya Bello ya musanta rahoton cewa ‘yan bindiga sun yi yunkurin hallaka shi.

Gwamnan jahar Kogi a Najeriya Yahaya Bello
Gwamnan jahar Kogi a Najeriya Yahaya Bello © Kogi state
Talla

Wannan na nufin Yahaya Bello ya karyata kalaman kwamishinan yada labarai na jihar Kigsley Fanwo, Wanda ya fara bayar da labarin cewa ‘yan bindigar sun budewa kwambar motocin gwamnan wuta cikin daren Lahadi akan hanyarsa ta Abuja.

Sai dai a wani taron manema labarai da gwamna Yahaya ya yi a birnin tarayyar kasar Abuja, ya musanta cewa ‘yan bindiga sun far masa, yana mai cewa kwambar motocin wani babban mutum ne ta yi karo da nasa ayarin.

Yace wannan ne ya tayar da hatsaniya tsakanin jami’an ‘yan sandan da ke tsaron sa da kuma wasu sojoji da ke aiki a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar, don haka babu wani labarin ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ce abin takaici ne yadda aka danganta jami’an tsaro da ke aikin tabbatar da zaman lafiya da ‘yan bindiga.

Gwamna Bello ya kuma sha alawashin ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya kan aikin da suke yi na tabbatar da tsaro, yana mai cewa tabbas hakan na amfanar jama’ar Kogi kwarai da gaske.

Hare-haren ‘yan bindiga musamman a arewacin Najeriya ba sabon abu bane, sai dai a iya cewa rahoton cewa ‘yan bindigar sun farwa jami’an gwamnati basu cika yawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.