Isa ga babban shafi
Zaben Liberia

Weah da Boakai na gumurzun karshe a Talatar nan a Liberia

A wannanTalatar al’ummar Liberia ke sake fita rumfunan zabe don kada kuri’unsu a zagaye na biyu na fafatawa tsakanin shugaban kasar mai-ci, George Weah da kuma abokin hamayyarsa, Joseph Boakai.

Joseph  Boakai tare da George Weah
Joseph Boakai tare da George Weah AFP
Talla

Shugaba Weah da tsohon mataimakin shugaban kasar, Boakai sun yi fafatawa mai zafi a zagayen farko na zaben, amma babu wanda ya samu fiye da kashi 50 na kuri’un da aka kada a cikinsu, lamarin da ya tilasta zuwa zagaye na biyu.

Weah wanda tsohon shahararren dan kwallon kafa ne, ya samu kashi 43.83, yayin da Boakai ya samu kashi 43.44 a zagayen farkon.

Wannan gajeruwar tazarar da ke tsakaninsu a sakamakon zagayen farko, na nuni da yadda zagaye na biyu na gobe Talata zai yi matukar zafi kamar dai yadda masharhanta suka bayyana.

Su biyu ne kadai za su yi gwajin kwanji a zagaye na biyun sabanin zagaye na farko wanda ‘yan takara 18 suka fafata da juna.

Shugaba Weah da Boakai na fatan samun karin magoya baya daga wadan can jam’iyyu 18 da suka fice daga cikin takarar tun a zagayen farko.

Fafatawar ta dai, maimaicin abin da ya faru ne tsakanin manyan ‘yan takarar biyu a shekarar 2017, lokacin da suka sake haduwa a zagaye na biyu wanda shugaba Weah ya lashe a wancan lokacin bayan ya samu kashi 61.54 na kuri’un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.