An kaddamar da yakin neman zaben shugabancin Jamhuriyar Demokradiyar Congo
An kaddamar da yakin neman zabe a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo har na tsawon wata guda ranar Lahadi, kafin babban zaben da ke tafe cikin watan Disamba.
Wallafawa ranar:
'Yan takara 26 cikin har da shugaba mai ci Felix Tshisekedi ke fafatawa a neman shugabancin kasar, daidai loakcin da gabashin kasar ke fama da hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai.
Kimanin masu kada kuri’a miliyan 44 ne suka yi rajista, daga cikin al’ummar kasar kusan miliyan 100, da za su zabi shugaban kasa a ranar 20 ga watan Disamba.
Za kuma su zabi tsakanin ‘yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi a kasar mai dumbin albarkatun kasa, amma rikece-rike da cin hanci da rashawa ya yi mata katutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu