Isa ga babban shafi

Bikin baje kolin kasa da kasa na masana'antun kayan tsaro da soja (EDEX 2023) A Masar

Masar tana karbar bikin baje kolin kasa da kasa karo na 3 na masana'antun kayan tsaro da na soja (EDEX 2023) daga 4 zuwa 7 ga Disamba.Za a gudanar da baje kolin ne a cibiyar baje kolin kasa da kasa ta birnin Alkahira karkashin jagorancin shugaban kasar Abdel Fattah Al-Sissi, babban kwamandan sojojin kasar Masar, sama da kamfanoni 400 daga kasashe 46 ne ke halartar taron.

Daya daga cikin motocin yaki kirar Faransa a bikin baje kokin Eurosatory a arewacin Faransa ranar  14 ga watan Yuni na shekarar  2022.
Daya daga cikin motocin yaki kirar Faransa a bikin baje kokin Eurosatory a arewacin Faransa ranar 14 ga watan Yuni na shekarar 2022. AP - Michel Euler
Talla

Tariq Al-Khatib, shugaban sashen fasaha na cibiyar bincike ta kasa da kasa ta Masar, ya bayyana cewa, tare da dukkan abubuwan da ke faruwa a halin yanzu, kasashe da dama na kokarin tabbatar da tsaronsu, musamman a fannin sa ido, da kiyaye na'urori da kuma kayyade kan iyakokin kasar.

Daya daga cikin masana'antu masu kera kayan yaki da Soja
Daya daga cikin masana'antu masu kera kayan yaki da Soja AP - MOHAMED EL-SHAHED

Ya ƙunshi rumfuna 22 da ke wakiltar ƙasashe da suka haɗa da Amurka, China, Indiya, Faransa da Jamus.

Manyan kamfanoni da suka kware a tsarin tsaro  suma suna nan, daga tsaron iska zuwa  da tsaro ta yanar gizo.

A kan tsayawarsa, Ciro Granato, wakilin Santor Security, ya gabatar da wata na'ura da aka sani da "Mai kare Maganar Harp". Manufar ita ce a rage haɗarin satar bayanan sirri  na yayin ganawar ido-da-ido da kuma hana sauraran bayanai an kera na'urar ne domin gwamnatoci da wasu kamfanoni su yi amfani da ita, kuma a yanzu shugabanni da firaministan kasashe da dama ne ke amfani da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.