Isa ga babban shafi
ZABEN CONGO

Matsalolin tsaro a Jamhuriyar Congo na kara tabarbarewa gabanin zaben kasar

Al’amuran tsaro na ci gaba da tabarbarewa a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, lamarin da ya jefa rayuwar ‘yan gudun hijirar da ke rayuwa a sansanonin da ke kusa da yankin cikin zulumi, yayin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da babban zabe a wannan wata na Disamba.

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyya Congo, Félix Tshisekedi, yayin wani gangamin yakin neman zabe a Kinshasa,ranar 19 ga Nuwamba, 2023.
Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyya Congo, Félix Tshisekedi, yayin wani gangamin yakin neman zabe a Kinshasa,ranar 19 ga Nuwamba, 2023. © Samy Ntumba Shambuyi / AP
Talla

Kasar da ke tsakiyar Afirka mai fama da rikici, wadda kuma ke dauke da arzikin ma’adanai, al’ummarta da dama, musamman mazauna gabashi na ganin cewa gwamnati ta wofintar da su.

Chantal Uwimana, wadda ta tsere zuwa yankin Masisi, daga yammacin Goma, ta ce ta gaza yin rijistar katin zabe domin samun damar kada kuri’a a zaben 20 ga Disamba, saboda matsalar tsaro.

Gabashin Congo dai na fama da matsalar masu dauke da makamai, yakin da ya bazu a yankin tun daga shekarun 1990.

Daga cikin kungiyoyin masu dauke da makaman akwai akwai M23 da suka kwace ikon wasu yankuna tun a karshen shekarar 2021, abin da ya tilastawa sama da mutum miliyan guda barin muhallansu.

Kungiyar likitoci ta kasa-da-kasa ta fitar da rahoton cewa, dubban mutane ne ke ci gaba da tserewa daga Arewacin Kivu.

Shugaba Felix Tshisekedi, mai shekaru 60, wanda ke neman wa’adi na biyu, ya sha alwashin dakile matsalolin tsaro.

Sai dai bayan shekaru biyar yana mulkin kasar, lamuran a Janhuriyar Dimokardiyyar Congo sun kara tabarbrewa fiye da baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.