CAF, ta nada El Hadji Diouf, Asamoah Gyan, Ahmed Hassan da Augustine 'Jay-Jay' Okocha a matsayin jakadunta
Shahararun zakarun tarihin kwallon kafar nahiyar Afrika irinsu El Hadji Diouf, Asamoah Gyan, Ahmed Hassan da Augustine 'Jay-Jay' Okocha sun kasance sunayen farko da aka nada jakadun hukumar kwallon kafar nahiyar Afrika Caf a karkashjin wani sabon shirin da aka kirkiro.Rawar da za su taka, ta ta’allaka ne wajen kokarin zaburar da ci gaba ga hukumar CAF, da kuma inganta yanayin kwallon nahiyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Haka kuma za su taka muhimmiyar rawa a cikin wasu ayuka masu muhimmanci da suka hada da shirya kwambalar, tare da tafiyar da sabon shirin ayukan jinkai, harakokin kasuwanci da kuma na kyautata jin dadin rayuwar al’umma da dai sauransu.
Tsarin da aka bi wajen zaben wadannan kwararu a fannin kwallon kafar da suka bar tarihi mai armashi, da kuma suka kasance mutane ne da aka sani cikin jama ;a sosai, bai takaita kawai daga kwarewar da suka samu a fannin kwallon kafar kwararu kawai ba, ya hada ne da kasuwanci da kuma irin matsayin da suke da shi ne a cikin al’umma.
Diouf, sau biyu yana sabe gambin dan wasa mafi kwarewa na hukuma CAF Awards, na ci gaba da tsayawa a cikin kwakwale sakamakon namijin kokarin da ya yi a kungiyar Lions de la Teranga du Sénégal. Tare da kyakywan tarihin kurciyar da ya bari a 2000 a kwata final na gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekara ta 2002 tare da buga wasan kwata final na gasar cin kofunan duniya a kasashen Coréa ta kudu da Japon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu