Isa ga babban shafi

MDD za ta kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya a Congo nan da karshen shekarar 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan da karshen watan Afrilu mai zuwa akalla dakarunta 2000 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin gabashin Jamhuriyar damukradiyar Congo ne za su fice daga kasar. 

Dakarun MINUSCO a Congo
Dakarun MINUSCO a Congo REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Wannan dai ne mataki na farko da ta shirya dauka wajen janye ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar mai fama da rikice rikice. 

A cikin watan Disamban shekarar bara ne Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da batun kawo karshen zaman dakarun a Congo, biyo bayan bukatar da Shugaba Felix Tshishekedi ya gabatar a cikin watan Satumba, kan batun gaggauta janye dakarun wanzar da zaman lafiyar a kasarsa. 

Akalla dakarun MINUSCO dubu 13,500 aka jibge a kasar tun daga shekarar 2010 dan taimakawa wajen tabbatar da tsaro a yankin gabashin Jamhuriyar Damukradiyar Congo.

Dakarun MONUSCO a gabashin Jamhuriyar Damukradiyar Congo
Dakarun MONUSCO a gabashin Jamhuriyar Damukradiyar Congo © AFP - Guerchom Ndebo

Jagorar shirin, Bintou Keita, ta shaidawa manema labarai cewa daga lardin kudancin Kivu za a kwashi kashin farko na dakarun, sannan ta ce sansanonin Majalisar Dinkin Duniya 14 dake fadin kasar za su koma karkashin ikon jami'an tsaron kasar ta Congo. 

Daga bisani dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake lardin arewacin Kivu da Ituri za su fice daga kasar baki daya. 

Ministan harkokin wajen Congo Christophe Lutundula ya shaidawa manema labarai a birnin Kinsasha cewa ana sa ran sauran dakarun su kammala ficewa kafin ranar 31 ga watan disamba shekarar 2024 dinnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.