Isa ga babban shafi

CPJ ta koka da karuwar garkame 'yan jaridu a kasashen Afrika

Kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta CPJ ta koka da yadda matsalar take hakkin ‘yan jaridu ke ci gaba da ta’azzara a yankin kudu da saharar nahiyar Afrika, bayan karuwar adadin ‘yan jaridun da gwamnatocin kasashen yankin ke jefawa a gidan yari.

Eritrea ce kasa mafi yawan garkame 'yan jaridu a kasashen na kudu da saharar Afrika.
Eritrea ce kasa mafi yawan garkame 'yan jaridu a kasashen na kudu da saharar Afrika. DS
Talla

Alkaluman da CPJ ta fitar ta ce adadin ‘yan jaridar da gwamnatocin kasashen suka jefa a gidan yari ya karu daga ‘yan jarida 31 da aka kai gidan yari a 2022 zuwa 47 a 2023, lamarin da ta bayyana a matsayin mai tayar da hankali lura da yadda ake ci gaba da take hakkin fadar albarkacin baki.

CPJ ta ce Eritrea ce kasa mafi yawan garkame ‘yan jarida a yankin cikin 2023 da yawan ‘yan jarida 16 kuma ita ke matsayin ta 7 a duniya baki daya wajen take hakkin ‘yan fafutukar tabbatar da ‘yancin fadar albarkacin bakin.

A cewar CPJ galibi Eritrea kan garkame ‘yan jaridar na lokaci mai tsawo ba tare da gabatar da su gaban kotu don amsa tuhuma ba kasancewar babu wani laifi da gwamnatin kasar za ta iya tuhumarsu da aikatawa.

Kasa ta biyu a wannan yanki ita ce Habasha da yawan ‘yan jaridu 8 sai Kamaru mai 6 sannan Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.