Isa ga babban shafi

Turai na cikin tsaka mai wuya saboda matakin Nijar da Mali da Burkina Faso

Kungiyar Tarayyar Turai na cikin tsaka-mai-wuya dangane da ci gaba da  zamanta a Mali da sauran kasashen yankin yammacin Sahel bayan ta ki hada kai da  Rasha wajen fadada ayyukan sojinta a yankin.

Babban Jami'in Diflomasiyar Kungiyar EU, Josep Borell.
Babban Jami'in Diflomasiyar Kungiyar EU, Josep Borell. AP - Jean-Francois Badias
Talla

Babban Jami’in Diflomasiyar Kungiyar Turai, Joseph Borell ya bayyana haka gabanin wani taro da ministocin tsaron Turai za su gudanar a birnin Brussels, yayin da ya bayyana cewa, matakin da gwamnatocin sojin Mali da Burkina Faso da Nijar suka dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS  ya kara sukurkuta manufar EU ta zama a Sahel.

Mista Borell ya kara da cewa, lallai wannan matakin da kasashen uku suka dauka ya ja hankali, wanda ke zuwa a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada karfinta na fada-a-ji a Sahel.

Babban Jami’in na Diflomasiyar ya ce, tuni Rasha ta yi karfi a Mali kuma nan kusa za ta sake yin karfi a Nijar da Burkina Faso.

Yanzu haka Kungiyar Tarayyar Turan ta EU na da wa’adin nan da ranar 24 ga watan Mayu mai zuwa da ta yanke shawara kan ko dai ta ci gaba da zama a Mali ko kuma akasin haka kamar yadda Borell ya ce.

Kungiyar Turai ta jaddada cewa, ba ta son hada kai da Rundunar African Corp ta sojojin Rasha wadda ta maye gurbin dakarun Wagner a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.