Isa ga babban shafi

Gobara ta kashe mutane da lalata motoci da kadarori na kasuwanci a Nairobi

Akalla mutane uku ne suka mutu yayin da wasu fiye da 270 suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi a wata babbar mota dauke da iskar gas a babban birnin kasar Kenya.

Gobara a Nairobi na kasar Kenya
Gobara a Nairobi na kasar Kenya REUTERS - THOMAS MUKOYA
Talla

Fashewar a cewar mai magana da yawun gwamnati Isaac Maigua Mwaura, gobarar ta kara lalata motoci da dama da kuma kadarori na kasuwanci. “Abin takaici, gidajen zama a unguwar suma sun kone kurmus.

Barnar da gobara ta yi a Nairobi
Barnar da gobara ta yi a Nairobi REUTERS - MONICAH MWANGI

 

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Douglas Kanja ya shaida wa manema labarai cewa akalla mutane uku ne suka mutu sannan 271 aka kwantar da su asibitoci daban-daban a birnin Nairobi. Gobarar ta tashi ne a cikin daren jiya Alhamis a unguwar Embakasi a kudu maso gabashin babban birnin kasar. Hotunan da kafafen yada labaran kasar suka yada sun nuna wutar ta kama gidaje da dama. Felix Kirwa, wani direban tasi ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa ya dawo gida ne lokacin da ya ji karar fashewar wasu abubuwa guda biyu da ya sa gidansa ya girgiza tare da farfasa tagar.

 

Fashewar Gas a Nairobi
Fashewar Gas a Nairobi REUTERS - MONICAH MWANGI

 

Wannan dai bas hi ne karo na farko da aka ta ba samun irin wannan gobara, ko a  shekarar 2018, wata gobara da ta tashi a kasuwar Gikomba ta Nairobi ta kashe mutane 15 tare da jikkata akalla 70. Tara daga cikin wadanda suka mutu suna cikin wani gida ne da ke kusa da kasuwar yayin da wasu shida,ciki har da yara hudu  suka mutu sakamakon raunukan da suka samu a asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.