Isa ga babban shafi

Babbar kotun Kenya ta haramta tura 'yan sandan kasar yaki da 'yan daba a Haiti

Babbar kotun Kenya ta dakatar da shirin gwamnatin kasar na aika ‘yan sandan ta zuwa Haiti karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, batun da ya haddasa cece-kuce, tare da maka gwamnatin gaban kotu.

'Yan sandan Kenya,
'Yan sandan Kenya, © Tony Karumba / AFP
Talla

Akalla ‘yan sandan Kenya dubu guda ne gwamnatin kasar ta amince za ta aikasu Haiti don gudanar da aikin yaki da matsalar daba da rikice-rikicen da suka dabaibaye kasar, sai dai tun bayan gabatar da shirin, bangaren adawa ya kalubalanci batun tare da maka gwamnatin gaban kotu.

Tun farko kotun ta dakatar da aikin tura ‘yan sandan wadanda aka tsara za su tafi zuwa Haiti a farkon watan nan kamar yadda aka cimma tsakanin gwamnatin ta Kenya da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka amince a watan Oktoban bara.

Sai dai babar kotun ta Kenya a yau juma’a karkashin jagorancin mai shari’a Chacha Mwita ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da damar iya yin gaban kanta wajen fitar da kowanne irin jami’in tsrao daga kasar don aikin wanzar da zama lafiya a wata kasa face sai da sahalewar ilahirin bangarorin gwamnati bisa cikakken tsarin da doka ta tanada.

A cewar mai shari’a Mwita duk wani yunkuri da ya kaucewa neman sahalewar bangarorin kai tsaye ya sabawa kundin tsarin mulkin Kenya.

Dag abara zuwa bana dai kungiyoyin ‘yan daban na Haiti sun hallaka akalla mutane dubu 5 baya ga tilastawa wasu dubu 200 barin matsugunansu, dalilin da ya sanya majalisar dinkin duniya neman ‘yan sanda daga kasashe don girke su a kasar ta yankin Caribbean da nufin wanzar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.