Isa ga babban shafi

Babbar kotun Kenya ta haramtawa gwamnati tura 'yan sanda zuwa Haiti

Yayin da majalisar dokokin kasar Kenya ta sahalewa gwamnati aika ‘yan sanda 1,000 zuwa kasar Haiti, domin taimaka magance matsalar ‘yan daba da suka addabi kasar da ke yankin Karebiya, babbar kotun kasar ta dakatar da wannan yunkuri.

Wani dan sandan Kenya kenan yayin wani sintiri lokacin wata zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a Nairobiranar 19 ga Yuli, 2023.
Wani dan sandan Kenya kenan yayin wani sintiri lokacin wata zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a Nairobiranar 19 ga Yuli, 2023. © AFP / LUIS TATO
Talla

Babbar kotun wanda tun farko ta hana yunkuri a watan Oktoba, ta kara fadada matakinta ta hanyar daile yunkurin gwamnatin kasar tura jami’an tsaro zuwa Haiti, a wani shirin wanzar da zzaman lafiya na kasa da kasa.

Tsohon dan takarar shugabancin kasar kuma lauya, Ekuru Aukot, shine ya gabatar da korafin gaban kotun, inda ya bayyana shirin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a matsayin babban kuskure da gwamnati za ta tafka, musamman wajen asarar rayukan jami’an tsaron Kenya.

Alkalin kotun mai shari’a, Chacha Mwita, ya ce zai sanar da sabon hukuncin da kotun ta yanke a ranar 26 ga watan Janairu mai zuwa, duk dai da nufin dakile wannan yunkuri.

Matakin dai ya zo ne, sa’o’I bayan da Majalisar dokokin kasar Kenya ta amince da bukatar gwamnati na tura dakarun zuwa Haiti, sai dai ‘yan adawa sun soki wannan mataki, inda suka sanya alamar tambaya kan inda za a samo kudaden da za a kasha domin aiwatar da wannan aiki, daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.