Isa ga babban shafi

Jami'an 'yan sanda a Najeriya sun kama wani Boka, da ake zargi da cin zarafin dabbobi

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wani mutum da ake zargin boka ne da amfani da dabbobi ba bisa ka’ida ba, da kuma yi musu kisan gilla da azabtar da su, da sunan tsafi.

Nigerian Police Officer.
Nigerian Police Officer. CGTN Africa
Talla

Wannan ya biyo bayan kiraye-kiraye da ‘yan kasar suka rika yi shafukansu na X kan yadda mutumin ke wallafa irin kisan gillar da yake yiwa dabbobi da suna asiri.

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu da ke kudancin kasar ta ce mutumin mai suna Nnabuikem dan asalin kauyen Ovoko da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta kudu, yayi kaurin suna wajen wallafa bidiyon cin zarafin dabbobi dake tayar da hankali.

Bokan da yayi fice a shaffin Facebook ya dora alhakin wannan ta’adda kan masu zuwa neman sa’a a wajen sa, yana mai jadadda cewa ta hanyar yiwa dabbobin wannan salon kisa ne kadai za’a iya samun sa’a a aikin asirin da yake yi.

Wani bidiyo na baya-bayan nan da ya fi daukar hankali shine yadda aka ga mutumin yana daga hawainiya da mage a cikin turmi da rayukan su, yayin da yake karanto surkulle.

A bayanin da rundunar ‘yan sanda ta yi a shafinta na X ta ce ta samu kiraye-kiraye daga jama’a da ke kokawa kan wannan ta’adda mai daga hankali don haka ta yanke shawarar kama mutumin, kuma nan ba da jimawa zata gurfanar da shi a gaban kotu.

Tuni dai kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dabbobi suka yaba da wannan kamu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.