Isa ga babban shafi

Rikicin Jamhuriyar Congo na daga cikin wadanda aka yi watsi da su a duniya - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa halin da ake ciki na jin kai a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya kara tabarbarewa, ciki kuwa har da matsalar cin zarafin mata da ke kara kamari.

Yadda 'yan gudun hijira ke fita neman abinci a garin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo kenan.
Yadda 'yan gudun hijira ke fita neman abinci a garin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo kenan. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Shugaban sashen kula da ayyukan jin kai, a ofishin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Bruno Lemarquis, ya shaida wa taron Majalisar ta kafar bidiyo cewa, rikicin da ke faruwa a kasar yana daya daga cikin mafi muni, rikitarwa da dadewa.

Ya ce munanan tashe-tashen hankula tsakanin kungiyar M23 da dakarun kasar Congo ya yi kamari, wanda ya haifar da mummunan kalubale ga ayyukan jin kai da kuma gudun hijira.

Kiran na baya-bayan nan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin nan da karshen shekara.

Fiye da mutane miliyan 25 ne ke cikin tsananin bukatar agajin jin kai don tsira, sannan sama da miliyan bakwai rikicin ya raba da muhallansu a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar.

Har ila yau, a halin yanzu kasar na fama da mummunar ambaliyar ruwa da ta shafi mutane miliyan 2 da larduna da dama a fadin kasar.

Gabashin Congo dai ya shafe shekaru yana fama da tashe-tashen hankula, inda kungiyar ta M23 a cikin kungiyoyi sama da 100 masu dauke da makamai ke fafatawa a yankin da ke da arzikin ma'adinai wanda ya yi iyaka da Rwanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.