Isa ga babban shafi

Chadi ta tsayar da ranar gudanar da babban zaben kasar

Hukumar zaben Chadi ta ce a ranar 6 ga watan Mayun wannan shekarar ce za a gudanar zaben shugaban kasar, wanda zai kawo karshen mulkin soji da Mahamat Idriss Deby Itno ke jagoranta na tsawon shekaru 3 da rabi.

Ma'aikatan zabe yayin kirga kuri'a a zaben shekarar 2016 a N'Djamena.
Ma'aikatan zabe yayin kirga kuri'a a zaben shekarar 2016 a N'Djamena. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Bayan kashe tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno da ‘yan tawaye suka yi, Mahamat Deby ya amshi ragamar kasar tare da alkawarin gudanar da zabe cikin watanni 18, sai dai shugaban ya kara shekaru 2 akai, kafin a tsaida lokacin gudanar da zaben.

A baya dai ya sheida wa kungiyar Tarayyar Afrika cewa ba zai tsaya takara ba, amma bayan kwas-kwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar a tsakiyar watan Disambar bara, jam’iyyar da ke mulkin kasar MPS ta tsaida shi a matsayin dan takararta, lamarin da ya sanya ‘yan adawar kasar bukatar ya janye daga takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.