Isa ga babban shafi

Tsohon jagoran 'yan tawayen Laberiya ya daukaka kara kan hukuncin kisa

Tsohon jagoran tawayen Liberia, Kunti Kamara, ya daukaka kara kan hukuncin kisa da wata kotu a birnin Paris ta yanke masa tun 2022,  sakamakon kama shi da laifukan cin zarafin dan adam da aikata laifukan yaki.

Tsohon jagoran 'yan tawayen Laberiya ya daukaka kara kan hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa
Tsohon jagoran 'yan tawayen Laberiya ya daukaka kara kan hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa © RFI
Talla

A ranar 2 ga watan Nuwamban 2022 kotun a Faransa ta yankewa Kamara hukuncin kisa saboda kama shi da laifin cin zarafin dan adam da bakin zalinci kan fararen hula a kasar.

Kamara ya aikata wannan laifi ne a shekarar 1993 da 1994 a waje da cikin kauyen Foya da ke lardin Lofa na arewa maso yammacin Liberia.

Kunti Kamara, shine shugaban kungiyar tawaye ta United Liberation Movement of Liberia for Democracy, kungiyar da ta rika tafka yaki da dakarun gwamnati karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Charles Taylor.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.