Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar sojojin Guinea su jinkirta mika mulki ga farar hula

Sabon Fira Ministan Guinea ya yi nuni da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Kasar a shekarar 2021 na iya jinkirta  mika mulki ga farar hula har zuwa shekarar 2025.

Shugaban gwamnatin sojin Guinea Kanar Mamadi Doumbouya.
Shugaban gwamnatin sojin Guinea Kanar Mamadi Doumbouya. AP
Talla

Amadou Oury Bah, wanda gwamnatin sojin kasar ta nada shi makwanni biyu da suka wuce, shi ne jami’in gwamnatin kasar na farko da ya fara nuni da cewa sojojin na iya jinkirta mika mulki a karshen shekaraar 2024 kamar yadda aka tsara.

Kungiyar kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ce ta matsa wa gwamnatin sojin Guinea lamba a kan shirya gudanar da zabe kafin karshen wannan shekarar, amma  kuma akwai alamar tambaya a game da yiwuwar hakan, duba da yadda babu wani ci gaba a game da mika mulkin, da kuma rikice-rikicen cikin gida.

Fira ministan ya shaida wa tashar Radio France Internationale a ranar Talata cewa akwai shirye -shirye da dama da suke yi a game da mika mulki, kuma baya ga matsin tattalin arziki, dole ne a yi aikin tabbatar da karshen rikicin siyasar da ya addabi kasar.

Guinea, wadda ke fama da talauci duk kuwa da yalwar albarkatun kasa, ta sha fama da mulkin kama karya tsawon gwamman shekaru, kana tana fuskantar matsalar  karancin makamashi da wutar lantarki.

Sabon fira ministan ya musanta cewa sojojin da ke mulkin kasar na neman dawwama a kan madafun iko, yana mai cewa masu mulkin kasar Guinea na bukatar kasar ta koma cikin hayyacinta.

Yankin yammacin Afrika ta fuskanci yawaitar juyin mulki tun daga shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.