Isa ga babban shafi

Annobar yunwa ta afkawa kasashen yankin kudancin Afrika- USAID

Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ta yi gargadin fadawar akalla mutane miliyan 20 cikin tsananin yunwa a kasashen kudancin Afrika sakamakon annobar farin da ya afkawa yankin cikin shekarar nan.

Wasu al'ummomin kasashen yankin kudancin Afrika.
Wasu al'ummomin kasashen yankin kudancin Afrika. © AFP/Tony Karumba
Talla

Alkaluman da USAID ta fitar game da halin yunwar da al’ummar kasashen Zimbabwe da Malawi da kuma Mozambique baya ga Madagascar za su fuskanta ta nuna cewa al’ummomin kasashen 4 na kudancin Afrika baza su iya ciyar da kansu a shekara mai kamawa ta 2025 ba, sakamakon farin da suka fuskanta da ya hana noma.

Hukumar ta bayyana cewa tun a watannin farko na shekarar nan kasashen biyu suka fara tsananin bukatar agajin abinci, kari kan tallafin da yanzu haka suke karba daga hukumomi irin USAID da ma shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya musamman a yankunan karkara na Zimbabwe wadanda yanzu haka suka dogara kacokan kan tallafin abinci.

A cewar hukumar duk da wannan agaji akwai mutum miliyan 2 da dubu 700 da ke tsananin bukatar agajin abinci a Zimbabwe kadai, inda tuni makwabtan kasar irin su Zambia da Malawi suka ayyana halin da ake ciki da annoba.

Alkaluman na USAID sun ce yanzu haka annobar yunwar ko kuma farin ya ci gaba da tsananta a kasashen Botswana da Angola baya ga Mozambique da Madagascar wadanda suka fara fuskantar annobar farin tun a shekarar 2023.

Bayanai sun nuna cewa kasashen yankin na Kudancin Afrika na fama da matsalar gajeruwar damuna wadda ke hana iya gudanar da harkokin noma yadda ya kamata lamarin da ke kaiwa ga asarar amfanin gona ko da an shuka, maimakon samun yabanya me kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.