Isa ga babban shafi

MDD ta kaddamar da asusun tallafawa Burundi bayan tsanantar ambaliya

Gwamnatin Burundi da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya sun kaddamar da asusun neman tallafi ga kasar wadda ke fuskantar zubar ruwan sama ba kakkautawa fiye da wata guda wanda ya haddasa mummunar ambaliyar da ta raba mutane fiye da dubu 100 da muhallansu.

Wani yanki a Burundi.
Wani yanki a Burundi. Uganda Red Cross Society
Talla

Kakkarfan ruwan da kasashen gabashin Afrika ke fuskanta a makwannin baya-bayan nan ya kai ga mutuwar akalla mutane 58 a Tanzania wasu 13 a Kenya wanda ya tilasta kaddamar da asusun tattara kudaden tallafin don agazawa kasashen, musamman Burundi wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na sahun kasashe 20 da ke tsananin bukatar agaji.

Yanzu haka ruwa ya cika ilahirin manyan titunan birnin Bujumbura, bayan da damuna ta fadi a kasar tun cikin Satumban bara, kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu mummunar ambaliyar ta shafi mutane dubu 203 da 944 yayinda mutane dubu 96 suka rasa matsugunansu.

A cewar Majalisar yanzu haka mutane dubu 306 na tsananin bukatar agaji a sassan Burundi baya ga wasu dubban daruruwa a makwabtan kasar Tanzania da Kenya wadanda suma ambaliyar ruwan ta tagayyara.

Burundi ke matsayin kasa mafi talauci yanzu haka, hasashen da masanan suka yi na nuna cewa ruwan zai ci gaba da zuba babu kakkautawa har zuwa watan Mayu wanda ke nuna bukatar da ake da ita wajen samun kudaden tafiyar da ayyukan jinkai a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.