Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Daular Larabawa, Oman da kuma Bahrain
Saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ɗauke da iska mai ƙarfi, da suka haddasa ambaliyar ruwa a sassan kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ya tilasta wa babban filin jiragen saman birnin Dubai karkatar da jirage da dama da a baya aka tsara za su sauka a birnin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ruwan saman mai ƙarfi, ya kuma haddasa ambaliyar ruwan a sassan Bahrain da kuma ƙasar Oman, inda rayukan mutane 18 suka salwanta a tsakanin ranakun Lahadi zuwa Litinin da suka gabata.
A birnin Dubai, ruwan saman mai ɗauke da iska mai ƙarfi ya tilasta dakatar da sauka da tashin jiragen sama na tsawon mintuna aƙalla 25, kafin lamurra su daidaita.
Bayanai sun ce jiragen da ke neman tashi daga katafaren filin nasu da ke birnin na Dubai ne kaɗai suka riƙa zirga-zirga da yammacin jiya, suma ɗin sai da suka riƙa fuskantar tsaiko saboda yadda motoci ba sa iya ratsa hanyoyin da ke kai wa da filin jiragen, biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye su.
A ƙasar Oman kuwa, ambaliyar ruwan rayukan mutane 18 ta lakume, cikinsu kuma har da wasu kananan yara ‘yan makaranta da wasu manya uku, bayan da ambaliyar ta yi awon gaba da motar da suke ciki a ranar Lahadin da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu