Isa ga babban shafi

EU ta bukaci gudanar da bincike akan manyan kaburbura da aka samu a asibitocin Gaza

Kungiyar Tarayyar Turai ta goyi bayan kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi game da gudanar da bincike mai zaman kansa kan wasu manyan kaburbura makare da gawarwaki da aka gano a asibitocin Zirin Gaza da sojojin Isra’aila suka lalata.

Yayin  da ma'aikatan lafiya ke zakulo gawarwaki a wani asibiti da ke Khan Yunis
Yayin da ma'aikatan lafiya ke zakulo gawarwaki a wani asibiti da ke Khan Yunis AFP - -
Talla

Mai magana da yawun Kungiyar Tarayyar Turai, Peter Stano ya bayyana cewa, wannan al’amari ne da ya tilasta su  har suka bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin take dokokin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.

Yana da matukar muhimmanci a gudanar da sahihin bincike mai zaman kansa domin tabbatar da abin da ya faru a cewar EU.

Ofishin Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce,  ya kamata a shigar da kwararrun  masu bincike na kasa da kasa a yayin gudanar da tuhumar.

Ofishin ya ce, ya kadu matuka da yadda aka yi rugu-rugu da asibitocin Gaza biyu mafi girma da suka hada da Al-Shifa da Nasser.

Sai dai tuni sojojin Isra’ila suka musanta zargin da ake yi musu na binne gawarwakin mutanen, inda suka bayyana zargin a matsayin mara tushe ballantana makama.

Sojojin sun kara da cewa, sun kashe kimanin ‘yan tawaye 200 tare da gano wasu tarin makamai a yayin samamen da suka kaddamar a asibitin Al-Shifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.