Isa ga babban shafi

Hamas ta ce wakilanta na hanyar zuwa Masar don tattaunawar tsagaita wuta

Hamas tace wakilanta za su yi balaguro zuwa ƙasar Masar don ci gaba da tattaunawar laluɓo yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza a wannan Asabar da farar aniya, a yunƙuri na baya-bayan nan na neman dakatar da yaƙin da take gwabzawa da Isra’ila yau kusan watannni 7.

Shugaban Hamas, Ismaïl Haniyeh.
Shugaban Hamas, Ismaïl Haniyeh. MAHMUD HAMS / AFP
Talla

 

Masu shiga tsakani na ƙasashen waje na sauraron martanin Hamas a game da tayin tsagaita wuta ta kwanaki 40, tare da musanyar waɗanda aka yi garkuwa da su da fursunoni Falasɗinawa da ke zaman kaso a Isra’ila.

A wata sanarwa da ta wallafa shafin intanet ɗinta, Hamas ta jaddada aniyarta ta cimma tsagaita wuta  a  Gaza, tana mai cewa waƙilanta za su halarci tattaunawa a Masar.

Sai dai a ranar Juma’a, sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken ya zargi Hamas da kawo cikas ga ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

An sha samun tasgaro a cikin watannin da aka shafe ana neman cimma tsagaita wuta a Gaza sakamakon buƙatun da Hamas suka miƙa, waɗanda suka haɗa da neman cimma tsagaita wuta  na tsawon lokaci, kuma fira ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya sha alwashin kakkaɓe jauron mayaƙan Hamas a Rafah.

Amma a jiya Juma’a Blinken ya jaddada adawar da Amurka ke yi da batun kutsawa Rafah ta ƙasa da Isra’ila ke shirin yi, yana mai cewa har zuwa wannan lokaci, Isra’ila ba ta miƙa mata shirin da ta yi na kare fararen hula ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.