Isa ga babban shafi

Ambaliya ta kashe mutane 50 a Somaliya tare da raba dubu 700 da muhallansu

Ambaliyar ruwa a Somaliya ta kashe mutane 50 tare da raba kusan dubu 700 daga gidajensu, kamar yadda wani jami'in gwamnatin kasar ya sanar, inda ake fargabar ruwan sama mai karfi da ya fara a ranar Talata zai kara dagula al'amura a kasar.

Yadda ambaliyar ruwa ta shafi wani yanki na kasar Somaliya. 6/11/23
Yadda ambaliyar ruwa ta shafi wani yanki na kasar Somaliya. 6/11/23 REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Yankin na kahon Afirka na fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya da ke da nasaba da sauyin yanayi na El Nino, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukan mutane tare da raba da dama da muhallansu, ciki har da kasar Somaliya, inda ruwan sama ya lalata gadoji tare da mamaye gidaje.

Hotun birnin Baida dake kasar Somaliya
Hotun birnin Baida dake kasar Somaliya AFP - YASUYOSHI CHIBA

"Mutane 50 ne suka mutu a wannan bala'in... yayin da ta tilastawa sama da 687,235  barin gidajensu," in ji daraktan hukumar kula da bala'o'i ta Somalia, Mohamud Moalim Abdullahi a wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Ya kara da cewa " ruwan sama da ake sa ran za a yi tsakanin ranakun 21 zuwa 24 ga watan Nuwamba... na iya haifar da ambaliyar ruwa da za ta iya haddasa mutuwa da barna."

Wani yaro a wata anguwar da ambaliya ta mamaye a Somaliya. 6/11/23
Wani yaro a wata anguwar da ambaliya ta mamaye a Somaliya. 6/11/23 REUTERS - FEISAL OMAR

A ranar Asabar, hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta ce adadin mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa a Somaliya "ya kusan ninki sau biyu a cikin mako guda", yayin da mutane miliyan 1.7 ke fama da bala'in baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.