Isa ga babban shafi
Palasdinu

Palesdinawa na gudanar da zanga-zangar neman ‘Yanci

Dubun dubatar Palesdinawa ne suka yi gangami a yankin gabar yamma da Kogin Jodan domin nuna goyon bayansu ga bukatar neman tabbatar da ‘yancin Palesdinu.Ana tunanin zanga-zangar zata zarce har zuwa ranar Juma’a lokacin da Shugaba Abbas zai gabatar da kudurin Palesdinawa ga Ban Ki-moon Sakatare Janar na Majalisar Dunkin Duniya.A yankin Ramalla daruruwan mutane ne suka yi gangami domin nuna goyon bayansu tare da kira ga kasashen duniya su amince da ‘yancin kasar Palesdinu.A lokacin da take gabatar da jawabi, Gwamnan yankin Ramalla Leila Ghanam ta bukaci kasashen duniya su amince da ‘yancin Palesdinu, domin alkawali ne da suka dauka tsawon shekaru 60 da suka gabata.Tana danganta wannan kiran ne, dangane da matsayar da kasashen 181 suka cim ma a Majalisar Dunkin Duniya a watan Nuwabar shekarar 1947.Masu gudanar da zanga-zangar, sun hada da Musulmi, da Kirista dauke da tutar Palesdinu, da kuma Tutar kungiyar Fattah ta shugaba Mahmoud Abbas 

Palesdinawa a yankin Ramallah masu gudanar da zanga-zangar neman 'yancin Palesdinu
Palesdinawa a yankin Ramallah masu gudanar da zanga-zangar neman 'yancin Palesdinu REUTERS/Ammar Awad
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.