Isa ga babban shafi
Saudiya

Mata zasu fara kada kuri’a a Saudiya

A yau ne maza ke kada kuri’ar zaben kananan hukumomi a Saudiya, zabe na karshe da mazan zasu kada kuri’a ba tare da Mata ba, bayan amincewa da dokar da zata bai wa Mata damar kada kuria a zabukan kasar.Maza sama da Miliyan 1 ne suka yi rijista domin kada kuri’a, sai dai an samu rashin fitowar mazan bayan bude runfunan Zabe, musamman a tsakiyar birnin Riyadh.An dade dai Mata a Saudiya na yakin neman halatta masu kada kuri’a a zaben Saudiya,tare da neman ‘Yancinsu tun bayan haramta masu tukin mota ko tafiya ba tare da wani namiji ba.A Makon nan ne Sarki Abdalla ya bada sanarwar amincewar Mata su kada Kuri’a, tare da amincewa da matan a Majalisar Shura. Matakin da kasashen Amurka da Birtaniya suka yi na’am da shi.A bangaren Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta yi na’am da matakin amma tace gwamnatin Saudiya na tafiyar Hawainiya wajen tabbatar da ‘yancin Mata.  

Matan Saudiya suna gudanar Sallar Jam'i
Matan Saudiya suna gudanar Sallar Jam'i © Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.