Isa ga babban shafi
Faransa

An yanke wa wasu mata 2 hukunci kan saka Hijabi a Faransa

A karon Farko wata kotu a kasar Faransa, ta yanke hukunci kan wasu mata biyu da aka samu da laifin sanya Hijabi dake rufe daukacin fuska bayan haramta saka Hijabin a bainar Jama’a.Wadanan mata biyu da aka samu da laifin sanya Hijabi, sun hada da Hind Ahmad, mai shekaru 32, da aka ci tarar Euro 120, da kuma Najat Nait Ali, mai shekaru 36, da aka ci tarar kudi Euro 80.Wannan shi ne karo na farko da wata kotu a kasar ta yanke hukunci kan masu sanya Hijabi, tun bayan sanya hannu kan dokar da shugaba Nicolas Sarkozy ya yi.Yann Gre, na kungiyar da ke kare kundin tsarin mulki, da ke kare matan biyu, yace zasu daukaka kasar zuwa kotun kasashen Turai, muddin aka tabbatar da hukuncin a kansu.Matan Musulmi sama da 2,000 ke sanya Hijabi, daga cikin Musulmi kusan miliyan shida dake kasar faransa.  

Dokar hana saka Nikafi a Faransa
Dokar hana saka Nikafi a Faransa Reuters / Stéphane Mahe
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.