Isa ga babban shafi
UN-Palestine

Palesdinawa: mun samu kuri’u 8 a kwamitin Sulhu

Ministan harakokin wajen Paledinawa yace sun samu kuri’u takwas a kwamitin Sulhu a kudirinsu na neman cikakken wakilci a Majalisar Dunkin Duniya, inda suke neman Karin kuri’a daya kacal.A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Ramalla, riyad Maliki yace sun samu tabbaci daga kasashen Najeriya da Gabon inda suka ce zasu kada kuri’ar amincewa da ‘yancin Palesdinu.Daga cikin kasashen da suka tabbatarwa Palesdinu kuri’;ar amincewa sun hada da kasar Rasha da China da Indiya da Africa ta Kudu da Brazil, sai kuma Karin tabbaci daga Nigeria da kasar Gabon.A cewar Maliki suna kokarin sasantawa da kasar Bosniya da Colombiya da Portugal domin samun amincewarsu.Yanzu haka shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas ya shirya gudanar da ziyara a kasashen Columbia da Portugal da Hunduras a watan Octoba.A ranar Juma’a ne Shugaba Abbas ya gabatar da kudurin Palesdinu a zauren taron Majalisar Dunkin Duniya, tare da neman goyon bayan kasashen duniya ga ci gaban kudirin. Sai dai kasar Amurka tace zata toshe kudirin na Palesdinu ko da sun samu kuri’un da suke bukata.Kasahen Turai da kasar Amurka sun nemi gabatar da kudurin neman sasantawa tsakanin Palesdinawa da Isra’ila, matakin da suke tunanin zai karye kwarin gwiwar dakatar da kudurin PalesdinuA yanzu haka kuma Pelesdinawa sun ce babu wata tattaunawa da zata sake hada su da Isra’ila illa tabbatar da ‘yancinsu, amma Isra’ila ta yi na’am da tayin tattaunawar na kasashen Turai da Amurka. 

shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas,
shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas, REUTERS/Darren Whiteside
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.