Isa ga babban shafi
Afganistan

Bukin cika shekaru 10 da yakin Amurka a Afganistan

A yau ne ake gudanar da bukin cika shekaru 10 da kaddamar da yakin Amurka da kawayenta a kasar Afganistan. Ana gudanar da bukin ne cikin tsauraran matakan tsaro bayan jerin hare haren da ake kai wa a cikin kasar da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.An baza jami’an tsaro a Kabul babban birnin kasar da ke fama da hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar tsohon shugaban kasar Burhanuddin Rabbani, da gwamnatin kasar ta nada jagoran sasanta zaman lafiya da Kungiyar Taliban.Al’ummar kasar Afganistan da dama ne ke neman ficewar dakarun Amurka da kawayenta daga cikin kasar bayan sun gudanar da zanga-zanga a jajibirin bukin.Amurka da kawayenta sun kaddamar da yakin ne domin fatattakar Taliban don cafke shugaban Al Qaeda Osama bin Laden da Amurka ke zarginsa da kai harin 11 ga Watan Satumba. Wani hari da Amurka ta kai a shekarar 2001 ya tarwatsa sansanin kungiyar Al Qaeda a Afganistan.Tun bayan kai harin watan Satumba Amurka ta kaddamar da jerin hare hare a birnin Kabul da sauran sassan yankunan kasar. 

Jami'an tsaro da aka baza a  Kabul
Jami'an tsaro da aka baza a Kabul REUTERS/Omar Sobhani
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.