Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Isra’ila da Hamas zasu yi musayar Fursunoni

Isra’ila da Kungiyar Hamas sun amince da yarjejeniyar musayar fursunoni, abinda zai kai ga sakin sojin Isra’ila Gilard Shalit da aka kama kusan shekaru shida, yayin da Israila zata saki Palasdinawa 1,027 da ta ke rike da su.Prime Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana farin cikinsa da yarjejeniyar, inda yace nan bada dadewa ba Shalit zai koma gida, a karkashin wannan yarjejeniya da Masar ta jagoran ta.An cafke Gilad Shalit ne a sakamakon wani hari da Hamas ta kai a Isra'ila a shekarar 2006, kuma tun bayan kama shi ne batun ya ja hankalin al’ummar Isra'ila.Khaled Meshall na kungiyar Hamas, yace cikin Palasdinawa 1,027 da Isra’ila zata sake, 27 daga cikinsu mata ne. 

Hoton Sojan Isra'ila Gilad Shalit.
Hoton Sojan Isra'ila Gilad Shalit. REUTERS/ Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.