Hamas ta mikawa Isra’ila shalit ta hannun hukumomin Masar
Kungiyar Hamas ta mikawa dakarun Isra’ila Shalit ta hannun hukumomin Masar masu shiga tsakanin yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da palesdinu.Tuni aka saki Palasdinawa 477 da Isra’ila ke tsare da su a gidan yari. Sama da Fursunoni 1,000 ne kuma ake sa ran Isra’ila zata saki bayan mika mata Gilad Shalit.A shekarar 2006 ne kungiyar Hamas ta kama Gilad Shalit bayan kaddamar da yaki.Tun da safiyar yau Talata ne Hamas ta dauki Gilad Shalit zuwa Rafah yankin da ke tsakanin Gaza da Masar domin mika shi ga wakilan Isra’ila.A watan gobe ne Isra’ila zata saki sauran fursononin Palesdinu Bayan sakin wasu daga cikinsu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Dr Sadiq Alkafawi a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu