Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Isra’ila zata gina sabbin gidaje a yankin Falesdinawa

Gwamnatin Isra’ila tace zata gina sabbin gidaje 2,000 a Yankunan Palasdinawa, yayin da kuma zata katse harajin da ake bai wa Palasdinawan.A wani taro da Majalisar Ministocin kasar ta gudanar, a karkashin jagorancin Fira Minista Benjamin Netanyahu, shugaban ya amince da shirin, a matsayin mayar da martani kan amincewa da Palasdinu a kungiyar UNESCO.A ranar litinin ne hukumar UNESCO da ke kula da al’adu ta Majalisar Dunkin Duniya ta amince da wakilcin Falesdinawa bayan da wakilan hukumar suka kada kuri’ar amincewa.Tuni Amurka da Isra’ila suka bayyana janye tallafin da suke bai wa UNESCO kusan rabin kasafin kudin hukumar. Kuma Amurka ta yi gargadin sauran hukumomin Majalisar Dunkin akan matakin da UNESCO ta dauka.Sai dai kuma Hamas ta yi Allah waddai da matakin da Isra’ila ta dauka, a matsayin mayar da martani kan amincewa da ita a matsayin wakiliya a UNESCO.Mai Magana da yawun Mahmud Abbas, Nabil Abu Rudeina, yace amincewa da gina sabbin gidaje 2,000 wani shiri ne na Isra’ila na watsi da sasantawa, tare hanawa Palasdinawa haraji.     

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Reuters/Jack Guez
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.