Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta karrama Jong-un matsayin wanda zai gaji mahaifin shi

Hukumomin Korea ta Arewa sun kara girma ga Kim Jong-Un wanda ake saran zai gaji mahaifinsa, yayin da kasashen Faransa da Jamus ke bukatar kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da kasar, bayan rasuwar shugaba Kim Jong-Il. Ministan harkokin wajen Faransa, Alain Juppe, yace suna zuba ido, da fatar cewar, wata rana mutanen Korea zasu samu yancinsu.

Marigayi Tsohon shugaban kasar Korea ta Arewa  Kim Jong-il da dansa wanda zai gaje shi Kim Jong-un (D).
Marigayi Tsohon shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong-il da dansa wanda zai gaje shi Kim Jong-un (D). Reuters/Yonhap
Talla

Gwamnatin kasar Korea ta Arewa ta ware kwanaki 13 domin juyayin mutuwar shugaba Kim Jong-Il wanda ya mutu a ranar Assabar sanadiyar ciwon Zuciya.

An kwashe kwanaki biyu ba tare da bayyana mutuwar Shugaban ba, kafin wata Sanarwa da kafar Telebijin a kasar ta bayar tare da kiran ‘al’ummar kasar bada goyon bayansu ga yaronsa Kim Jong-un.

Tun bayan mutuwar mahaifin, ake tunananin Jong-un zamaninsa ya fara na shugabancin kasar, inda masana a kasar suke ganin zai gudanar da mulki ne karkashin kulawar gwaggon shi da mijinta.

Kasar Amurka ta yi kiran samar da Zaman lafiyar a kasar Kora ta Arewa tare da neman sasantawa da kawarta Korea ta kudu.

An dade ana zaman Doya da Manja tsakanin Korea ta Kudu da Korea ta Arewa tun bayan kwashe shekaru uku ana yaki tsakaninsu inda kasar Amurka ta aika da dakarunta 28,500 a Kudancin Korea da wasu dakaru 50,000 a kasar Japan.

A ranar 28 ga watan Disemba ne za’a gudanar da Jana’izar shugaban a Pyongyang, ba tare da gayyatar wasu wakilan kasashen waje ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.